Bangaren siyasa: Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ahmadinejad ya bayyana cewa tunani irin na akidar Imperialismda kuma yadda yake hangen tarihi yana tattare da kuskure, domin kuwa wannan matattar akida ba za ta iya raya wata matattar akida ba.
Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga shafin shugaba hmadinejad na Iran cewa; tunani irin na akidar Imperialismda kuma yadda yake hangen tarihi yana tattare da kuskure, domin kuwa wannan matattar akida ba za ta iya raya wata matattar akida ba. Ahmadinejad ya bayyana hakan ne a wajen bude wani bankin hadin gwiwa tsakanin jamhuriyar musulunci ta Iran da kuma Venzuela, wanda ya halarta tare da takwaransa na kasar Venzuela Hogo Chavez, inda ya jaddada cewa karfin fada a ji na kasashe masu girman kai ya fara kawo karshe, abin da ke faruwa yanzu haka na matsalolin tattalin arziki da suka jawo wa duniya ya isa ya zama babban dalili kan hakan, amma ga sauran kasashe masu 'yancin siyasa suna da abubuwa da dama da za su iya yi domin ci gaban al'ummominsu ta fuskoki da dama, a siyasance da kuma bangaren bunkasa harkokinsu na tattalin arziki.
382288