IQNA

Iran Na Shirin Zama Mamba A Kwamitin Harkokin Ilimi Na Kasashen Musulmi

Bangaren siyasa: Cibiyar kula da harkokin ilimi da bincike kan hanyoyin karfafa tattalin arzikin kasashen musulmi ta bayar da bayani kan yuwuwar Iran ta zama mamba a cibiyar nan bad a jimawa ba.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; cibiyar kula da harkokin ilimi da bincike kan hanyoyin karfafa tattalin arzikin kasashen musulmi ta bayar da bayani kan yuwuwar Iran ta zama mamba a cibiyar nan ba da jimawa ba. Shugaban bangaren kula da hulda da jama'a na majalisar shawara ta Iran ya bayyana cewa; kasantuwar Iran day ace daga cikin kasashen musulmi da suke taka rawa wajen yada ilimi na addini da ma na zamani tsakanin kasashen musulmi, ta cancanci ta zama mamba a wannan cibiya, ballantana idan aka yi dubi da irin rawar da take takawa ta fuskacin harkokin bunkasa tattalin arziki a tsakanin kasashen musulmi, ballantana uwa uba day ace daga cikin kasashe mambobi a kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC.

382285