IQNA

An Fara Gasar Karatun Kur'ani Ta Sojoji A Saudiyya

16:02 - April 06, 2009
Lambar Labari: 1761116
Bangaren kasa da kasa: An fara gudanar da gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa da ta kebanci sojoji a birnin Makka mai alfarma a karo na biyar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (Nasij) cewa; tun ranar Asabar da ta gabata ce aka fara gudanar da gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa da ta kebanci sojoji a birnin Makka mai alfarma a karo na biyar. Rahoton ya ci gaba da cewa yarima mai jiran gado a Saudiyya shi ne ya jagorantar gabatar da wannan gasa, inda daga karshe zai bayar da kyuta ta musamman ga wadanda suka yi nasara wajen cin gasar, yanzu haka dai sojoji daga kasashen musulmi da larabawa 19 ne suke halartar wannan gasa, inda suke gudanar da gasar a fagagen karatun kur'ani da harda da kuma ka'idojin karatun kur'ani wato tajwidi, gami ma'anonin ayoyin kur'ani da kalmomi. Babbar manufar gudanar da wannan gasa dai ita ce karfafa gwiwar sojoji da sauran jami'an tsaro na kasashen larabawa wajen mayar da hankali ga kur'ani da koyarwarsa.

382968



captcha