Bangaren kasa da kasa: An kafa wani kwamitin da zai gudanar da bincike kan ayyukan yaki da Haramtacciyar Kasar Isra'ila ta tafka kan al'ummar Gaza, wanda alkalin nan bayahude dan kasar Afirka ta kudu Richard Ganston zai jagoranta.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Faransa (AFP) cewa; Kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya kafa wani kwamitin da zai gudanar da bincike kan ayyukan yaki da Haramtacciyar Kasar Isra'ila ta tafka kan al'ummar Gaza, wanda alkalin nan bayahude dan kasar Afirka ta kudu Richard Ganston zai jagoranta. Richard Ganston wanda atsohon alkali ne kuma bayahude dan kasar Afirka ta kudu, ya shahara ta fuskacin gudanar da bincike kan ayyukan yaki, wanda kuma shi ne ya gudanar da bincike kan ayyukan yakin da aka aikata tsohuwar Ugoslavia, inda sabiya suka yi kisan kiyashi kan al'ummar musulmin Bosnia, ya bayyana cewa a wannan karon an dora masa nauyin gudanar da bincike kan yakin da Isra'ila ta kaddamar kan al'ummar Gaza, kuma ya tabbatar da cewa ba zai ji fargabar komai wajen gudanar da binciken kamar yadda aka nemi shi ya yi daga bangaren kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya.
383063