IQNA

Jami'ar Imam Sadiq (AS) Za Ta Fadada Bincike Kan Ilmomin Kur'ani

Bangaren fikra: Shugaban bangaren da ke kula da bincike a jami'ar Imam Sadiq (AS) da ke birnin Tehran ya bayyana cewa za su kara fadada ayyukan bincikensu kan ilmomin kur'ani da magabata suka rubuta, da nufin kara karfafa bincike daidai da bukatar zamanin da muke rayuwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; Babban darakta da ke kula da bangaren da ke kula da bincike a jami'ar Imam Sadiq (AS) da ke birnin Tehran ya bayyana cewa za su kara fadada ayyukan bincikensu kan ilmomin kur'ani da magabata suka rubuta, da nufin kara karfafa bincike daidai da bukatar zamanin da muke rayuwa. Ya kuma bayyana cewa daga cikin manufofinsu na yin hakan hard a kara fito da wasu ilmomin wadanda magabata suka rubuta, kuma har yanzu suke rubuce a cikin wasu tsoffin littafai da ba a karantawa, amma fitar da wadannan ilmomin tare da sake rubuta su a cikin wasu makaloli ko littafai na zamani zai taimaka wajen ilmantar da matasa da ma sawake ma masu gudanar da bincike kan wasu abubuwa da suka shafi ilmomin kur'ani ba tare da sun sha wahalkar neman sanadi daga wasu tsoffin littafai da aka rubuta kan hakan ba.

383102