Bangaren siyasa: Babban malamin addini kuma mataimakin shugaban majalisar koli ta mabiya mazhabar shi'a a kasar Labanan sheikh Abdul amir Qabalan, ya bukaci shugaban kasar Labanan day a kaurace wa zaman taro da shugabannin kasashen larabawa za su gudanar a kasar Libya a shekara mai zuwa.
Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga jaridar (Alsharq Alausat ) ta kasar Qatar cewa; malamin addini kuma mataimakin shugaban majalisar koli ta mabiya mazhabar shi'a a kasar Labanan sheikh Abdul amir Qabalan, ya bukaci shugaban kasar Labanan day a kaurace wa zaman taro da shugabannin kasashen larabawa za su gudanar a kasar Libya a shekara mai zuwa. Qablan ya bayyana cewa babban dalilinsa na yin wannan kira ga shugaban labanan din kuwa shi ne yadda gwamnatin Libya karkashin shugabancin Mu'ammar Gaddafi ta sace Imam Musa Sadr, tare da kin bayyana makomarsa sama da shekaru 30 da suka gabata, ya ce domin nuna wa gwamnatin Libya fushin al'ummar Labanan kan hakan ya kamata shugaban na Labanan ya kaurace wa zaman taron da shugabannin larabawa za su gudanar a birnin Tripoli a cikin shekara ta 2010. Tun a cikin shekara ta 1978 shugaban kasar Libya ya kirayi Imam Musa Sadr zuwa Libya, tun bayar isarsa kasar har inda yau take ba a kara jin duriyarsa ba tatre da abokan tafiyarsa.
382971