Daga Turkiya ne cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa labarin cewa: gidan talbijin na Al'alam da ke watsa shirye-shiryens ata hanyar tauraron dan adam ya watsa rahoton yadda al'ummar wannan kasa musamman a birnin Istambul suka gudanar da zanga-zangar kin jinin Amerika a daidai wannan lokaci na ziyarar da shugaban Amerika Barack Obama zai kai kasar.Masu zanga-zangar suna rera taken kai Obama ya kawo ziyara kasarmu dole ya fice daga Afganistan ya koma kasarsa kuma suna rera taken kin jinin Amerika da kungiyar tsaro ta Nato.
383149