Hujjatul Islama walmuslim Ja'afar Alawi Kiya shugaban ofishin jagora a jami'ar ilimi da fanni ta Hurramshahar a wata hira da cibiyar da ke kula da kur'ani a Iran Ikna ya bayyana cewa: matsayin kungiyoyi da bangarenci a Kur'ani mai girma yana da ma'anoni biyu .Ma'ana ta farko mummuna yayin da ta biyu mai kyau.Y kara da cewa; a cikin kur'ani kungiya da ta hada gungun mutane masu ta'assubanci da boye gaskiya da kin aiki da hankali da wahayi abin kama ce. Ya kuma bayyana ce amma kungiyar da ta kafu da wadanda suka kafa ta ked a burin isa ga kamala da aiwatar da ayyuka na alheri abin ruinguma da karba ce da hannnu biyuyu.
368648