Bangaren Manema labarai:Jalal Bitarafan: An canja kofofi biyar masu launin zinariya a Hubbarin Imam Huseini (AS).
A cikin rahoton bangaren manema labarai a cibiyar kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna bayan nakaltowa daga majiyar bada labarai ta Haimar Karim Al-ambari mamba a komitin bada tsaro a Hubbarin Imam Huseini (AS) ya bayyana cewa: sabo da yawan masu ziyartar wannan hubbari ne ya sa aka canja da fadada wadannan kofofi da hakan zai bawa masu kai ziyara damar walwala da ficewa ba cikin takurawa ba. Har ila yau ya kara da cewa akwai gini tsoho da tuni aka kamala gina sabo a gurbinsa.
383691