Bangaren kasa da kasa: Masanin harkokin tattalin arziki Joseph Stegaltez wanda ya samu kyautar zaman lafiya ta Nobel a shekara ta 2001, kuma shugaban kwamitin kula da harkokin tsarin tattalin arzikin duniya a Majalisar Dinkin Duniya, ya kirayi al'ummomin duniya da su yi amfani da tsarin tattalin arziki irin na musulunci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Clicanoo cewa; masanin harkokin tattalin arziki Joseph Stegaltez wanda ya samu kyautar zaman lafiya ta Nobel a shekara ta 2001, kuma shugaban kwamitin kula da harkokin tsarin tattalin arzikin duniya a Majalisar Dinkin Duniya, ya kirayi al'ummomin duniya da su yi amfani da tsarin tattalin arziki irin na musulunci. A cikin wani bayani da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar dangane harkokin tattalin arziki da kuma yadda za a kara inganta su a duniya, jami'in ya bayyana cewa bisa la'akari da matsalolin tattalin arziki da suka addabi duniya, a iyakacin saninsa da binciken da ya gudanar dangane da hanyoyin da ya kamata a bi wajen tunkarar wannan matsala, yin amfani da tsarin tattalin arzki na musulunci shi kadai ne mafita daga wannan matsala.
383544