Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet mallakin kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC cewa; Sakataren kungiyar ta OIC Ihsan Oglo zai halarci taron shekara-shekara na kasa da kasa da za a gudanar karo na biyu a birnin Santanbul na kasar Turkiya. Bayanin ya ce a wajen taron Ihsan Oglo zai gabatar da jawabai kan mahangar kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC dangane da muhimmancin da ke tattare da kusanto fahimta tsakanin al'adu da ma addinai a duniya. Taron dai zai samu halartar manyan baki daga sassa daban-daban na duniya da suka hada da Pir ministan kasar Spain Khozeh Luis Zapatero, da kuma babban sakataren majalisar Dinkin duniya Ban ki-moon, gami da shugaban kasar Amurka da a halin yanzu yake gudanar da ziyar aiki a kasar ta Turkiya, gami da shi kansa mai masafkin baki shugaban kasar ta Turkiya Abdallah Gol. Dukkanin manyan bakin dai za su gudanar da jawabai a wajen taron.
383591