IQNA

An Dora Alhakin Kusakuran A Rubutun Kur'ani A Kan Masu Buga Shi

14:40 - April 07, 2009
Lambar Labari: 1761570
Bangaren kasa da kasa: Shugaban kwamitin kula da ayyukan kur'ani na jami'ar Alazhar ta kasar Masar (Ahmad Almisarawi) ya bayyana cewa; kusakuran da ake samu a cikin rubutun kur'ani a wasu lokuta, ba kowa ke da alhakin hakan ba illa madaba'antun da suke buga kur'anan.
Kamfanin dillanci labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (Mohit) cewa ; shugaban kwamitin kula da ayyukan kur'ani na jami'ar Alazhar ta kasar Masar (Ahmad Almisarawi) ya bayyana cewa; kusakuran da ake samu a cikin rubutun kur'ani a wasu lokuta a kai a kai, ba kowa ke da alhakin hakan ba illa madaba'antun da suke buga kur'anan. Ya ce bai kamata ba a rika yawan samun kusakurai a cikin rubutun kur'ani mai tsarki, domin kuwa hakan na nuni ne da rashin kulawa yadda ta kamata daga bangaren madaba'atun da ke buga kur'anin, domin kuwa ya kamata ne a duba dukkanin rubutun kur'ani tun daga farko har zuwa karshe kafin buga shi, tare da yin la'akari da duk wani kuskure komai karancinsa domin gyara shi. Ya ce a bangare guda kuma nauyi ne da ya rataya kan gwamnatocin kasashen musulmi da ake buga kur'anai a cikin kasashen da su kafa kwamitoci masu sa ido kan yadda ake gudanar da aikin, domin kaucewa buga kur'ani da kuskure.

383680









captcha