IQNA

An Yi Allawadai Da Kisan Gillar Da Ake Yi Kan 'Yan Shi'a A Pakistan

14:39 - April 07, 2009
Lambar Labari: 1761572
Bangaren siyasa: Kakakin ma'aikatar harkokin wajen jamhuriyar Musulunci ta Iran ya yi Allawadai da kisan kiyashin da ake yi kan mabiya mazhabar shi'a a kasar Pakistan a masallatai da suke gudanar ayyukan ibada.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; a wata zantawa da ya yi da manema labarai jiya a birnin Tehran, Kakakin ma'aikatar harkokin wajen jamhuriyar Musulunci ta Iran ya yi Allawadai da kisan kiyashin da ake yi kan mabiya mazhabar shi'a a kasar Pakistan a masallatai da suke gudanar ayyukan ibada. Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Hassan Qashqawi ya kara da cewa babu wani dalili da zai sanya a kai hare-hare kan wuraren ibada wata kila ma da sunan jihadi a tafarkin Allah, ya ce masallaci wurin bautar Allah ne, duk wanda ya je wurin kuma yana bautar Allah, saboda haka kai irin wannan hari lallai aiki ne na assha, kuma Iran tana yin Allawadai da hakan da kakkausar murya.

383643







captcha