Bangaren zamantakewa: Wakilin jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran a birnin Madina mai alfarma ya jaddada wajabcin hadin kan al'ummar musulmi a wannan lokaci domin fuskantar makircin da makiya Musulunci suke kulla wa musulmi a ko'ina cikin fadin duniya.
Kmafanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet mallakin hukumar kula da ayyukan haji da Umra ta kasar Iran cewa; wakilin jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran a birnin Madina mai alfarma ya jaddada wajabcin hadin kan al'ummar musulmi a wannan lokaci domin fuskantar makircin da makiya Musulunci suke kulla wa musulmi a ko'ina cikin fadin duniya. Hojjatol islam (Najaf Najfi Rohani) ya bayyana hakan ne jiya a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a gaban wasu mutanen iran da suke da niyar tafiya kasa mai tsarki domin gudanar da ayyukan umra, ya kara da cewa duniyar musulmi na bukatar hadin kai a wannanzamani fiye da lokutan baya, domin kuwa addinin Musulunci na fuskantar barazana daga makiya musamman ma yahudawan sahyuniya da 'yan barandansu, wadanda suka sha alwashin dusashen hasken addinin Musulunci, wanda kuma kawo karshen wannan makirci nasu na bukatar hadin kan al'umma ne.
383484