IQNA

Za A Gudanar Da Gasar Karatun Kur'ani A Kasar Tanzania

14:38 - April 07, 2009
Lambar Labari: 1761574
Bangaren Kur'ani: Za a fara gudanar da gasar karatun kur'ani a kasar Tanzania domin share fagen halartar babbar gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa da za a gudanar a birnin Tehran a cikin wata mai kamawa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; za a fara gudanar da gasar karatun kur'ani a kasar Tanzania domin share fagen halartar babbar gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa da za a gudanar a birnin Tehran a cikin wata mai kamawa. Rahoton ya ci gaba da cewa wadanda za su halarci gasar za su kara ne a fagagen kira'a da kuma harda, inda daga cikin wadnda suka samu nasarar wucew ne za a zabi wadanda za su wakilci kasar a gasar kasa da kasa da za a gudanar a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar Musulunci ta Iran. Rahoto ya kara da cewa za a zabo mutane biyar-biyar ne daga dukkanin bangarorin biyu na makaranta da kuma mahardata, kafofin yada labarai na kasar Tanzania za su watsa taron gasar kur'anin kai tsaye a cikin kasar.

383663




captcha