IQNA

Wasu Daga Cikin Yan Shi'a A Tailand Sun Gana Da Jakadan Iran A Wannan Kasa

Bangaren al'adu da zamantakewa: Wasu daga cikin yan Shi'a a kasar tailand sun gana da jakadan jamhuriyar musulunci a wannan kasa inda suka gabatar masa da rahoton ayyukan da suke gudanarwa.
Daga yankin ne cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa; a lokacin wannan ganawa da kuma tattaunawa da wani gungu na yan Shi'a da ke zaune a wannan kasa ta Tailand Hujjatul Islam Amiri wakilin jami'ar Almustapha(SW) Al'alami A Tailand da kuma tawagar amintattu da sheik Ahmad Kumi shugaban kungiyar bada taimakon alheri da kuma Sheik Gulamali Abazar limamin masallacin juma'a na Al-huda da kuma limamin Huseiniya ta imam Bara suka halarci wannan tattaunawa sun yi wa jakadan bayani dalla-dalla kan ayyukan da suke gudanarwa a wannan kasa.


384145