IQNA

Za A Horar Da Limaman Masallatai Kan Ilimin Kur'ani A Malasia

17:23 - April 08, 2009
Lambar Labari: 1762200
Bangaren kasa da kasa: Za a bayar da wani horo na musamman ga limaman masallatai a malasia kan ilimomin kur'ani mai tsarki da ya kamata su sani.
Kamfanin dillancin nlabaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran (BERNAMA) cewa; za a bayar da wani horo na musamman ga limaman masallatai a malasia kan ilimomin kur'ani mai tsarki da ya kamata su sani. Rahoton ya ci gaba da cewa babbar manufar bayar da horon dai ita ce sa limaman su samu cikakkiyar masaniya kan kur'ani da ilimominsa, kamar yadda hakan zai basu dammar ilmantar da su. Daga cikin muhimman abubuwan da wannan horo zai kunsa kuwa har da bangaren karatu, tare da sanin kai'dojinsa, gami da hardar kur'ani bisa matakai. Bangaren kula da harkokin addinin musulunci na jami'ar Malasia ne ya dauki nauyin gudanar da wannan bayar da horo ga limaman masallatn kasar.


384278

captcha