IQNA

Masu Tarjamar Kur'ani Kan Manta Da Bukatun Wadanda Ake Magana Da Su

17:22 - April 08, 2009
Lambar Labari: 1762218
Bangaren adabi: Shaharren marubuci kuma mai aikin fassara (Farid Javaher Kalam) ya bayyana cewa wasu lokuta masu tarjamar kur'ani sukan manta da abubuwan da mai karatu ko mai saurare ke bukata.
A cikin wata zantawa da ta hada shi da kamfanin dillancin labaran Ikna marubuci kuma mai aikin fassara dan kasar Iran (Farid Javaher Kalam) ya bayyana cewa wasu lokuta masu tarjamar kur'ani sukan manta da abubuwan da mai karatu ko mai saurare ke bukata. Ya ce sau da yawa salon da aka yi amfani da shi wajen fassara wata kalma ko jumla daga wani yare zuwa wani yare yak an yi tasiri wajen jan hankalin mai sauraro ko mai karantawa, wasu lokuta tasirin hakan yak an ja hankalinsa zuwa ga son ci gaba da sauraron ko karantawa, kamar yadda kuma wasu lokuta salon da aka yi amfani da shi wajen fassarar yak an sanya shi ya yi saurin gajiya wajen sauraro ko kuma karantawa, ta yadda har wasu lokuta yakan kosa. Marubucin ya ce wannan tasiri bai takaitu da tarjamar wasu littafai ko makalo ko abin da ya yi kama da haka ba, a a har ma da tarjamar kur'ani. A kan haka ya ce dole masu tarjamar kur'ani su yi la'akari tare dakiyaye hakan.

384292
captcha