Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (Alwasat) ta kasar Bahrain cewa; a mako mai zuwa ne za a fara gudanar da gasar kur'ani ta kasar Bahrain, inda makaranta da mahardata za su hallara domin shiga cikin gasar. Wadanda za su shiga cikin gasar za su kara ne a fagagen hardar dukkanin kur'ani da kuma juzu'i talatin sai kuma juzu'i goma sha biyar, kamar yadda gasar za ta tabo bangaren karatu da dukkanin nau'in kira'oi, sai kuma bangaren tafsiri inda za a yi tambayoyi dangane manonin ayoyi da kuma dalilan safkarsu, har ma tambayoyin za su hada da bangaren kissoshi da ke cikin kur'ani mai tsarki. Wannan dai shi ne karo na 10 da za a gudanar da wannan gasa a kasar Bahrain. Yanzu haka dai mutane 127 ne suka yi rijistar shiga kasar bangaren harda, sai kuma 160 da suka yi rijista a bangaren tajwidi.
384266