Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (Al-dastur) ta kasar Jordan cewa; sabon shugaban kasar Amurka Barack Hossein Obama, a cikin wani jawabi da ya gabatar a gaban majalisar dokokin kasar Turkiya ya bayyana cewa; Amurka ba ta gaba da addinin musulunci. Shugaban na Amurka ya bayyana hakan ne a kokarin da yake yi na kawo canji a cikin siyasar gwamnatin Amurka wadda tag abaci gwamnatinsa, wadda ta shahara da nuna tsananin gaba ga addinin musulunci. Obama ya ce dole ne a samu fahimtar juna tsakanin kasashen yammacin turai da kuma duniyar musulmi, domin kuwa a cewarsa sulhu da fahimtar juna tare da yin aiki kafada da kafada tsakaninsu shi kadai ne mafita. A bangare guda kuma ya jaddada wajabcin samara da zaman lafiya mai dorewa a yankin gabas ta tsakiya, kamar yadda ya nuna goyon bayansa kan batun kafa daular palastinu mai cin gishin kanta.
384242