IQNA

Dole Ne Duniyar Musulmi Ta Fadada Bincike Kan Kur'ani

17:20 - April 08, 2009
Lambar Labari: 1762222
Bangaren kasa da kasa: Binciken da aka gudanar a duniya kan ilmomin kur'ani idan aka kwatanta shi da binciken da aka gudanar a kan sauran littafai da aka safkar daga sama za a iya cewa ya yi karanci.
A wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran Ikna da farfesa Mohammad Abdulhalim malami a jami'ar London ya bayyana cewa; binciken da aka gudanar a duniya kan ilmomin kur'ani idan aka kwatanta shi da binciken da aka gudanar a kan sauran littafai da aka safkar daga sama za a iya cewa ya yi karanci. Ya ci gaba da cewa an gudanar da bincike da dama a littfan da aka safkar daga sama kamar Attaura da injila duniya, amma idan idan aka kwanta irin binciken da aka gudanar kan wadannan littafai da binciken da aka gudanar kan kur'ani, za mu samu cewa binciken da aka gudanar ko ake ci gaba da gudanarwa kan kur'ani ya gaza matuka. Ya ce dole ne kasashen musulmi ba da himma matuka wajen fadada bincike kan kur'ani tare da fitar da tarin ilmomin da ke cikinsa wadanda suke tattare da ci gaban dan adam, kama daga rayuwarsa ta duniya har zuwa rayuwar lahira.

384193
captcha