IQNA

ISESCO Za Ta Halarci Taro Kan Musulunci Da Ijtihadi A Faransa

Bangaren kasa da kasa: Hukumar da ke kula da yada ilimi da al'adu a Iran ISESCO zata halarci taron kasa da kasa kan musulunci da Ijtihadi da za a gudanar a Faransa.
Cibiyar da ke kula da harkokin Kur'ani a Iran Ikna ce ta nakalto daga bakin hukumar ta ISESCO cewa za halarci wannan taro na kasa da kasa da za a yi kan musulunci da ijtihadi a ffaransa da zai yi bincike kan abubuwa da dama da suka hada da kare hakkin dan adam a dokokin kasa da kasa da kuma dangantaka tsakanin musulmi da wanda ba musulmi bad a kuma Ijtihadi da matsalolin da yake fuskanta a tsakanin jama'a kuma Abdul Aziz Usman Altauwijari babban sakataren hukumar ta ISESCO zai bude wannan taro.

384837