IQNA

Manufa da Tsarin Iran Samar Da Hadin Kai A Yanki Da Ma Duniyar Musulmi Baki Daya

14:02 - April 09, 2009
Lambar Labari: 1762410
Bangaren siyasa: Shugaban majalisar shawara ta Iran a lokacin ganawarsa da ministan sadarwa kuma shugaban komitin zartarwa na Talbijin din Aljazeera ya bayyana masa karara cewa: manufa da tsarin Irann shi ne samara da hadin kai a tsakanin kasashen yankin da kuma duniyar musulmi baki daya.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa: a lokacin da Ali Larjani shugaban majalisar shawara ta jamhuriyar musulunci a Iran ke ganawa da Sheik Hamd bin Sami bin Khalifa Alsani ministan yada labarai da farfaganda na kasar Katar kuma shugaban komitin zartarwa na gidan Talbijin din Aljazeera ya bayyana masa manufa da tsarin Iran na neman hadin kai a tsakanin kasashen yankin da ma musulmin duniya a ko ina suke a doran kasa.Har ila yau ya jaddada masa burin Iran na samara da sulhu da kwaciyar hankali a tsakanin kasashen yankin da kuma musulmi duniya tare da warware duk wata matsala da ta shafi kasashen ba tare da coma bakin wata kasa ta wajen yankin ba .


384912
captcha