Bangaren kasa da kasa: Za a gudanar da taro kan musulunci da canje-canje zaman da suka yi daidai da shi, wanda aka ba take msulunci da ijtihadi, wanda za a gudanar birnin Paris na kasar Faransa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga majiyar kungiyar bunkasa ilimi da al'adun musulunci ta ISESCO cewa; za a gudanar da taro kan musulunci da canje-canje zaman da suka yi daidai da shi, wanda aka ba take msulunci da ijtihadi, wanda za a gudanar birnin Paris na kasar Faransa. Bayanin ya ci gaba da cewa taron na hadin gwiwa ne tsakanin kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adun musulunci ta ISESCO da kuma jami'ar Paris, amma an gayyaci wakilan kungiyoyi daban-daban na kasa da kasa da za su sa ido kan yadda taron zai gudana, kamar yadda aka gayyaci malaman addinin musulunci da ma masana musulmi da wadanda ba musulmi ba domin halartar taron. Babbar manufar gudanar da taron dai ita ce kara fito da mahangar musulunci dangane da abubuwa da dama da suka shafi lamurran da suke gudana a wannan zamani, domin wanke irin mummunar mahangar da wasu suke da ita a kan addinin musulunci musamman ma a kasashen yammacin turai.
384837