Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (Islam online) cewa; shugaban cibiyar musulmi na kasar Italia Mostafa Bastami ya bayyana cewa, tun bayan da suka samu labarin afkuwar girgizar kasa an kai mutane da dama zuwa asibiti domin ceto rayuwarsu wasu kuma sakamakon raunukan da suka samu sun rasa jinni, wannan ya sa musulmi da dama da ke yankin suka bukaci su bayar da gudunmawar jinni ga wadanda suke bukatar jinni daga cikin wadanda girgizar kasar ta shafa, inda suka bayar da jinni mai yawa domin taimaka wa masu bukuta, kamar yadda musulmin yankin bas u kafa a gwiwa wajen shiga cikin ayyukan ceto, domin tono mutanen da kasa ta danne, tare da kai wadanda suka samu raunuka zuwa asibiti cikin gaggawa, ya ce wannan ita ce koyarwar addinin msulunci.
384853