IQNA

Za A gudanar Da Gasar Hardar Hadisan Ma'aiki A Kasar Qatar

Bangaren kasa da kasa: Za a gudanar da gasar hardar hadisan ma'aiki a karo na goma sha hudu a kasar Qatar daga ranar Asabar mai zuwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (Al-sharq) ta kasar Qatar cewa; za afara gudanar da wannan gasa daga ranar Asabar mai zuwa, inda mahardata hadisan ma'aiki daga sassa daban –daban na kasar za su samu halarta, daga cikin mahalartan kuwa har da mata da kuma maza, masu matsakaitan shekaru. Babban alkalin da ke kula da wannan gasa (Salin Al-bakri) ya bayyana cewa; Wannan gasa za a gudanar da ita ne ta hanyar zabar wasu hadisai daga wasu littafai na musamman, wadanda tuni aka riga aka sanar da masu halartar gasar irin littafan da za su duba da kuma irin hadisan da za su hardace tare da fahimtar ma'anarsu, ya ce kafin zabar littfan da za a yi amfani da su wajen gudanar da wannan gasa, kwamitin da ke kula lamurran gasar baki daya ya tuntubi manyan malamai domin samun shawara daga gare su, inda daga karshe kuma aka cimma matsaya kan littafan da aka sanar da masu shiga cikin gasar, wadda ita ce irinta ta goma sha hudu da za a gudanar a kasar Qatar.

384854