Bangaren al'adu da fasaha: Za a gudanar da tarukan tunawa da zagayowar ranar shahadar shahid Mottahari a kasar India, inda za a bayar da wasu kayututtuka na musamman ga wasu mutane da suka taka rawar gani ta fuskoki da dama domin ci gaban addinin musulunci, wanda kuma wannan shi ne karo na biyu da ake gudanar da irin wannan taro tare da bayar da kyututtuka.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; nan da makonni uku masu zuwa za a gudanar da tarukan tunawa da zagayowar ranar shahadar shahid Mottahari a kasar India, inda za a bayar da wasu kayututtuka na musamman ga wasu mutane da suka taka rawar gani ta fuskoki da dama domin ci gaban addinin musulunci, wanda kuma wannan shi ne karo na biyu da ake gudanar da irin wannan taro tare da bayar da kyututtuka. Rahoton ya kara da cewa masana da daman e za su halarci taron daga sassa daban –daban na kasar India, daga cikin kyaututtukan da za a bayar har da allunan ban girma, da kuma kyaututtuka na kudi tsaba.
384947