Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto reshen kasar Jordan ya habarta cewa; cibiyar kula da yada addinin musulunci ta (Rasulullah Yuwahhiduna) ta kasar Jordan ta yi kakkausar kan yadda aka zabi pira ministan Danmark a matsayin babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO. Cibiyar ta sanar da hakan ne a cikin wani bayani da ta fitar, inda ta bayyana cewa kasar Danmark ta shahara wajen nuna gaba da addinin musulunci, inda take kallon wulakanta addinin musulunci ta hanyar cin zarafin manzon Allah (SAW) fadin albarkacin baki ne, kuma 'yancin bayyana ra'ayi ne, wanda hakan ke nuni da cewa kasar ba ta kallon addinin musulunci da musulmi da daraja, ballantana ta tausayawa musulmin da NATO ta jibge dakarunta a cikin kasashensu. A nasa bangaren Pira ministan kasar Turkiya Rajab tayyib Ardugan ya nuna rashin amincewarsa da zabar Pira ministan kasar danmark a matsayin sakataren kungiyar tsaro ta Nato, sakamakon furucin da ya yi kan cewa cin zarafin Manzon Allah (SAW) 'yancin bayyana ra'ayi ne.
384901