IQNA

Musulunci Bai Amince Da Wuce Gona Da Iri A Cikin Lamurra Ba

13:58 - April 09, 2009
Lambar Labari: 1762426
Bangaren fikira da ilimi: Al'ummar musulmi al'umma ce da kur'ani ya misilta ta da matsakaiciyar al'umma, kuma madaukakiya a cikin akida da dabi'u, ta yadda dukkanin ayyukanta sun ginu ne a kan koyarwar shari'a da hankali.
Kamfanin dillancin labaran Ikna reshen lardin Azarbaijan ya habarta cewa; a cikin wani bayani na hannuka mai sanda da bangaren kula da harkokin addini na lardin ya fitar, an bayyana cewa; al'ummar musulmi al'umma ce da kur'ani ya misilta ta da matsakaiciyar al'umma, kuma madaukakiya a cikin akida da dabi'u, ta yadda dukkanin ayyukanta sun ginu ne a kan koyarwar shari'a da hankali. A kan haka dole ne musulmi a kowane lokaci ya zama mai yin aiki da hankalinsa wajen gudanar da lamurransa na rayuwa ta yadda za su yi daidai da koyarwar addininsa. Kamr yadda kuma musulunci bai amince da wuce gonad a iri ba a cikin dukkanin lamurra, kama daga lamurra na addini har zuwa na rayuwar zamantakewa ta yau da kullum, hakan nan kuma bai amince da sakaci ko rashin kulawa da nauyin day a rataya kan mutum ba. A koda yaushe addinin musulunci yana dora dan adam kan sahihin tafarki ne da ya yi daidai da rayuwarsa, ba tare da nakasu ko wuce haddi ba.

384921




captcha