Bangaren kasa da kasa: A wani mataki na ci gaba da tsokanar mabiya addinin musulunci da wasu mutane ke yi a kasar Danmark, sun sake saka hoton nan na cin zarafin manzon Allah (SAW) da wata jaridar kasar ta yada a cikin shekara ta 2005.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya naklto daga kamfanin dillancin labaran kasar Faransa (AFP) cewa; wasu mutane a kasar Danmark, sun sake saka hoton nan na cin zarafin manzon Allah (SAW) da wata jaridar kasar ta yada a cikin shekara ta 2005, inda suka saka hoton a cikin shafukan internet da nufin kara yada a duniya. Kwamitin da ke kula ayyukan jaridu a kasar ta Danmark ya sanar cewa sama da hotuna torarci ga manzon Allah(SAW) dubu daya aka saka a cikin internet, inda ake sayar da kowane kwafi daya kudin yuro 188, kimanin dala 250 kenan. Da dama daga cikin kasashen musulmi da na larabawa sun nuna rashin gamsuwarsu da baiwa pira ministan kasar Danmark matsayin sakataren kungiyar tsaro ta NATO, sakamakon nuna halin ko in kula da cin zarafin addinin musulunci da jaridun kasarsa ke yi.
385595