IQNA

Za A Gudanar Da Taro Kan Kur'ani A Jami'ar Oxford

15:15 - April 11, 2009
Lambar Labari: 1763183
Bangaren kasa da kasa: Za a gudanar da wani taro mai taken Kur'ani da fduniyarmu ta yau a jami'ar Oxford ta kasar Birtania.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (Quan Institute) cewa; nan da watanni uku masu zuwa za a gudanar da wani taro kan ilmomin kur'ani, wanda aka sama take Kur'ani da duniyarmu ta yau. Bangaren kula da al'adun musulunci na kasar Iran ne ya shirya gudanar da wannan taro, tare da hadin gwiwa da jami'ar Oxford da ke Birnin London na kasar Birtaniya. Babbar manufar gudanar da wannan taro dai ita ce bayyana irin sakon da kur'ani yake dauke da shi ga dan adam, tare bayyana muhimman abubuwan da ya kamata al'ummomin nahiyar turai ya kamata su sani dangane da kur'ani, sabanin masaniyar da aka ba su kan shi, inda wasu daga cikin al'ummomin nahiyar turai musamman a cikin 'yan shekarun nan suke kallon addinin musulunci a matsayin addini na tashin hankali kamar yadda aka suranta musu. Taron zai bayyana kyakkyawar koyarwa irin ta kur'ani ga musulmi, da ma 'yan adam baki daya, inda masana daga kasashe duniya zasu gabatar da laccoci a wurin taron.



385671
captcha