Bangaren kasa da kasa: An fara gudanar da wani taron shekara-shekara na kungiyoyin musulmi na kasar faransa, da nufin tattauna muhimman batutuwa da suka yanayin zamantakewar rayuwa tsakanin mabiya addinin musulunci da sauran al'ummomi kasar Faransa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran (AFP) na kasar Faransa cewa; an fara gudanar da wani taron shekara-shekara na kungiyoyin musulmi na kasar faransa, da nufin tattauna muhimman batutuwa da suka yanayin zamantakewar rayuwa tsakanin mabiya addinin musulunci da sauran al'ummomi kasar Faransa. Wannan dai shi ne karo na 26 da kungiyar take gudanar da babban taronta na shekara-shekara, wanda yake samun halartar wakilan dukkanin kungiyoyin mabiya addinin musulunci na kasar Faransa, gami da wasu kasashen turai da ke makwaftaka da kasar. Inda ake gabatar da jawabai na wayar da kai ga musulmi da ma sauran al'ummomin kasar dangane da addinin musulunci gami da manufofinsa.
385627