Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa: jaridar Alkudus ta bada labarin cewa: Yahudawa masu tsauraran ra'ayin riko a gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a ranar asabar har zuwa lahadi za su rufe haramin Annabi Ibrahim a wani sabon yunkurin nuna kama da adawa da addinia wannan rana da ked a muhimmanci ga musulmi.Zaid Rabin Aljabari shugaban da ke kula da sha'anin addini bayan ya yi Allah wadai da wannan lamari ya bayyana cewa wannan mataki da yahudawan sahayoniya suka dauka ya kara fito da matsayin yahudawa na nuna adawarsu a fili kan addini.
385744