IQNA

Dila A Cikin Gida Kasuwar Baje Koli Kan Taimaka Yaran Gaza

Bangaren kasa da kasa: taro da aka ba shi sunan Dila Cikin Gida kan taimakwa kananan yara a yankin Gaza da aka fara a kasar Suriya.
Bayan ta nakalto daga kamfanin dillancin labarai na SANA cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa; Suzan Najamul Dine daya daga cikin wadanda suka shirya wannan taro ya bayyana muhimmancin wannan taro mai kayatarwa da kuma alfano domin ya shafi bangarori daban-daban na rayuwa da zaman takewa da kuma siyasa da kare hakkon bil adama musamman ma bisa la'akari da yadda haramtaciyar kasar Isra'ila suka yi kwanaki ashirin da biyu suna take hakkin mata da kananan yara a yankin Gaza na Palasdinu. A dayan bangare kuma zai yi magana kan yadda yara kanana suka nuna juriya da jarumtaka wajen tuntarar dakarun makiya da suka mallaki dukan karfi da makamai na zahiri amma suka rasa karfin ruhi da na zucciya da tausasawa.

386095