IQNA

Malummai A Afganistan Sun Jaddada Muhimman Kare Tsaro Da Sulhu A Cikin Gida

Bangaren siyasa da zamantakewa; komitin malummai a kasar afganistan ya bayyana muhimmancin tabbatar da hadin kai da sulhu a cikin gida a Afganistan tare da goyan bayan shugaban kasar Hamid Karzayi a wannan manufa.
Daga kasar afganistan ne cibiyar da ke kula da harkokin Kur'ani a Iran Ikna ta watsa labarin cewa; ta jiyo kafar wannan kasa na cewa komitin malummai a Afganistan yana goyan bayan manufar shugaban kasa da ke kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwaciyar hankali a wannan kasa har zuwa lokacin gudanar da zaben shugaban kasa da nay an majalisu a kasar. Shugaban komitin malummai a cikin wani bayani ne day a fitar ya bayyana goyan bayansa na taimakawa gwamnatin Karzayi a tshi fadin da ta ke yin a tabbatar da zaman lafiya a kasar kuma zaman lafiya da sulhu shi ne komi a kowa ce kasa a fadin duniya.

384048