Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Saphirnews cewa; a ranar lahadin wannan makon ce za a gudanar da taron matasa musulmi a birnin Paris na kasar Faransa a dandalin Mantes-la-Jolie, da nufin kalubalantar bakin dabi'u tsakanin matasan musulmi.
cibiyar ra'aya al'adu da bunkasa harkokin ilimi ta Turkawan kasar Faransa ce ta shirya gudanar da taron, da nufin fadakar da matasa musulmi kan muhimman abubuwan day a kamata su kiyaye wadanda suka yi karo da koyarwa irin ta addinin musulunci, wadanda kuma sun zama sun cakudu da al'adunsu kasantuwarsu suna rayuwa a cikin kasashen turai, kamar cudanya tsakanin maza da mata ba bisa ka'ida ba, da kuma shan giya gami da miyagun kwayoyi. Za a gayyaci masana domin gabatar da jawabai na hannunka mai sanda ga matasan.
386074