Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran (SPA) cewa; mai kula da bangaren hulda da jama'a na cibiyar kula harkokin addinin musulunci da gasar karatun kur'ani a kasar Saudiyya (Salman Omari) ya bayyana cewa; za a fara gudanar gasar hardar kur'ani ta share fage a kasar Saudiyya nan da 'yan makonni masu zuwa, da nufin tantance wadanda za su wakilci kasar a gasar karatu da hardar kur'ani ta duniya da za a gudanar a wannan shekara. Ya kara da cewa ciyar da ke kula da harkokin addinin musulunci da gasar karatu da hardar kur'ani a kasar Saudiyya ce ta dauki nauyin bayar da horo ga dukkanin matasa maza da mata da za su halarci gasar, inda samara musu da dukkanin abubuwan da suke bukata wajen tare da gogaggun malamai masu basu horo, yanzu haka dai kofa bude take ga sauran mutane da suke bukatar shiga cikin gasar domin rijist daga nan har zuwa mako mai zuwa.
386015