IQNA

A Jiya Ne Aka Fara Gudanar Da Gasar Hardar Kur'ani A Emarat

16:53 - April 12, 2009
Lambar Labari: 1763839
Bangaren kasa da kasa: An fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki a karo na goma a hadaddiyar daular larabawa, karkashin kulawar cibiyar kula da ayyukan kur'ani ta Ali maktum da kuma hukumar kula da harkokin addinin musulunci da birnin Dubai, wadda za a kwashe mako guda ana gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran (wam) na haddadiyar daular larabawa cewa; an fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki a karo na goma a hadaddiyar daular larabawa, karkashin kulawar cibiyar kula da ayyukan kur'ani ta Ali maktum da kuma hukumar kula da harkokin addinin musulunci da birnin Dubai, wadda za a kwashe mako guda ana gudanarwa.Rato ya ce gasar na samun halartar goggagun makaranta da mahardata kur'ani mai tsarki na kasar, tare da kuma alkalancin fitattun alkalan gasar kur'ani. Daya daga cikin wadanbda suka shirya gudanar da wannan gasa (Hamad Mohammad Abdulrahman) ya bayyana cewa; yanzu haka makaranta da mahardata da yawansu ya kai 210 da suke halartar taron, gami wasu kimanin 120 daga kasar Qatar, da suka hada da maza da mata. Bangarorin da ake gudanar da gasar kansu sun ahada da hardar dukkanin kur'ani, da kuma bangaren juzu'I 30, sai juzu'i goam sha biyar da juzu'i goma da kuma juzu'i biyar.

385957

captcha