Kamfanin dillancin labaran Ikan ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Saphirnews cewa; za a gudanar da taro mai taken kofa zuwa ga addinin musulunci a kasar Faransa a ranar lahadi mai zuwa wanda kuma shi ne karo na shida da ake gudanar da irin wannan taro. A wajen taron za a gabatar da laccoci dangane da mahangar addinin musulunci kan batutuwa da dama da suka shafi rayuwar dan adam, da nufin karfafa fahimtar musulmi kan addininsu da mahangarsa dangane da lamurran rayuwarsu ta zamantakewa. Rahoto ya kara da cewa masana gami da manyan malamai daga kasashe daban –daban ne za su halarci taron.
386083