Bangaren kasa da kasa: A ranar laraba ta gabata ce aka zabi birnin Njamina fadar mulkin kasar Chadi a matsayin birnin al'adun musulunci na nahiyar Afirka a shekara ta 2009.
Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga shafin internet na kungiyar bunkasa al'adu da ilimi ta kasashen musulmi ISESCO cewa; an zabi birnin Njamina fadar mulkin kasar Chadi a matsayin birnin al'adun musulunci na nahiyar Afirka a shekara ta 2009. Kungiyar ISESCO ta gayyaci tawagar gwamnatin kasar Chadi karkashin jagorancin ministan kula da al'adu da harkokin matasan kasar zuwa taron da za a gudanar na murnar zabar birnin a matsayin birnin al'adun musulunci a nahiyar Afirka a cikin shekara ta 2009, kamar yadda aka zabi biranan Bako na Azarbaijan da kuma Kualalampur na kasar malazia a matsayin biranan al'adun musulunci na nahiyar Asia, kuma za a gudanar da bukuwan ne a bai daya.
385987