Bangaren kasa da kasa: Sakataren tsaron kasar Birtaniya ya fadi cewa; musulmi daga cikin sojojin Birtaniya sun taka rawar gani da ta kamata wajen gudanar da ayyukansu.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet mallakin kamfanin dillancin labaran (mohit) cewa; sakataren tsaron kasar Birtaniya ya fadi cewa; musulmi daga cikin sojojin Birtaniya sun taka rawar gani da ta kamata wajen gudanar da ayyukansu. Ya ci gaba da cewa dole ne a samu sauyi na ci gaba a cikin rundunar sojin Birtaniya, kuma kasantuwar mutum musulmi ba zai hana shi shiga aikin soji a kasar ba. sakataren tsaron kasar Birtaniyan ya bayyana hakan ne a wajen wani taron sojin kasar, inda ya jaddada cewa musulmin kasar Birtaniya ba su da wata da dangantaka da ayyukan ta'addanci kuma bai kamata ma wani ya zarge da su haka ba. Yanzu haka akwai sojoji 390 musulmi a cikin sojin Birtaniya.
386774