Bangaren kasa da kasa: Musulmi za su iya sake zama al'umma guda daya matukar dai za su yi aiki da koyarwar addinin Musulunci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Bernama cewa; a wani taro da aka gudanar a babban masallacin juma'ar birnin Kualalampor na kasar Malazia kan matsayin ma'aiki (SAW) pira ministan kasar Abdallah Ahmad Badawi ya bayyana cewa; musulmi sun samu kansu cikin wani mawuyacin hali a yanzu, kuma babban ummul haba'isin hakan shi ne rarrabuwar kawunansu, ya ce da musulmi za su yi aiki da koyarwar addinin muslunci kamar yadda manzon Allah da kur'ani suka koyar da su, da sun sake zama al'umma guda cikin sauki. Pira ministan na kasar Malazia ya jaddada cewa dole ne musulmi su a jiye duk wani banbancin fahimta na mazhaba a tsakaninsu, domin dunke duk wata baraka a tsakaninsu, tare da yin aiki da koyarwar addini wadda ita ce ta hada su, da kuma hada gwiwa wajen isar da sakon addinin ga sauran al'ummomi.
386770