Bangaren kasa da kasa: Mujallar Human Events ta buga wani littafi mai suna (boyayyen Musulunci) tare da yada shi, da nufin ya saka matsananciyar gaba kan addinin Musulunci da musulmi a cikin zukatan Amurkawa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran Mohit cewa; mujallar nan ta Human Events da ake bugawa mako-mako a kasar Amurka, ta buga wani littafi mai suna (boyayyen Musulunci) tare da yada shi, da nufin ya saka matsananciyar gaba kan addinin Musulunci da musulmi a cikin zukatan Amurkawa. Rahoton ya ci gaba da cewa marubucin littafin wanda dan kasar Amurka ne maibiyin addinin kirista mai tsananin gaba da addinin musulunci Robort Sbister, ya bayyana addinin Musulunci a matsayin wani addini na tashin hankali da firgita dan adam, inda ya bayar da misalai kan kai hare-hare ta'addanci da wasu kungiyoyi da ke dangnata kansu ko abin da suke yi da addinin Musulunci, tare da bayyana hakan da cewa ita ce hakikanin koyarwa irin ta Musulunci. A wani bangaren littafin nasa ya bayyana cewa daya daga cikin manufofin musulmi a halin yazu ita ce kawar da Amurka baki daya daga doron kasa.
386761