IQNA

An Kawo Karshen Gasar Kur'ani Ta Sojoji A Kasar Saudiyya

15:59 - April 13, 2009
Lambar Labari: 1764387
Bangaren kasa da kasa: An kawo karshen gasar hardar kur'ani ta sojoji ta kasa da kasa da aka gudanar a birnin Makka mai alfarma da ke kasar Saudiyya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet mallakin kamfanin dillancin labarai na (Nasij) cewa; an kawo karshen gasar hardar kur'ani ta sojoji ta kasa da kasa da aka gudanar a birnin Makka mai alfarma da ke kasar Saudiyya. Rahoton ya ci gaba da cewa an kwashe mako guda ana gudanar da gasar wadda ta samu halartar sojoji daga kasashe 19 na kasashen musulmi da na larabawa, inda yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya Amir Sultan Bin Abdulaziz ya jagoranci guganar da wannan gasa da aka yi wa take da sunansa. An gudanar da gasar ne a fagen hardar da karatu, inda wasu suka kasance a bangaren hardar juzu'i 30, wasu bangaren hardar juzu'i 15, yayin da wasu kum abnagren hardar kur'ani baki daya, wasu a bangaren karatu da ka'idojinsa tajwidi. Amir Sultan Bin Abdul'aziz ya bayar da kyaututtuka ga wadanda suka halarci gasar, tare da bayar da wasu kyaututtukan na musamman ga wadanda suka lashe gasar.


386649
captcha