IQNA

Shugaban Kasar Iran Ya Girmama Kafafen Watsa Labarai Na Cikin Gida

Bangaren fasaha; Shugaban kasar iran ya jinjjina da yabawa kafafen watsa labarai na cikin gida a Iran kan taimakawar da suka yi a nasarorin da kasar ta samu musamman a makamashin nukliya.
Bayan ta nakalto daga bangaren hulda da jama'a na gidan radiyo da talbijin na kasar iran ,cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa labarin cewa: shugaban kasar Iran Mahmud Ahmadi Najad ya yaba da kuma jinjinawa kafafen watsa labarai na cikin gida da yadda suke gudanar da ayyukansu cikin nasara da ci gaban kasa ta dukan bangarori kama da al'adu ,zamantakewa,tattalin arziki da siyasa.Shugaban kasar ta Iran ya yaba da shirye-shirye da matakan da kuma goyan bayan da gidan radiyo da talbijin ke bawa shirin Iran kan makamashin nukliya na zaman lafiya don haka babu wani abu day a fice godiya da jinjinawa.

386745