Bangaren fasaha: Muhammad Rida Islamlu ya shirya wata Fim Kan kare hakkin dan adam da kuma ya yi cokaci kan yadda yahudawa ke take Hakkin Dan Adam kuma zai gabatar a gasar fina-fina ta aljazeera.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa: Muhammad Rida Islam lu ya shirya wannan fim din ce domin gabatar da ita a gasar Fina-finai ta Aljazeera inda a cikin wannan fim din ya fayyace biri har wutsiya kan yadda yahudawan sahayoniya ke take hakkin bil adama musamman mata da kananan yara fararen hula a yankuna daban-daban na palasdinu. Har ila yau a cikin wannan fim din ya yi bayyana kan abubuwa masu yawan gasket da haramtacciyar kasar isra'ila ke bi wajen takurawa fararen hula a Palasdinu.
386640