Ali Rida Salihi shugaban kula da yin Sallah a jami'ar Azad Islami a watan hira da cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ya bayyana cewa; wannan taro na kasa da kasa an shirya shi ne da zummar fahimtar juna da kara samun kusanci a tsakanin musulmi da kuma daliban jami'oin duniyar musulmi da kuma sanin matsalolin da ke addabarsu a zahiri da kuma hanyoyin magance su.Har ila yau ya kara da cewa; wannan taro zai taimaka matuka gaya wajen kara kusanci da sanayya a tsakanin musulmi.
386767