Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na middle east online cewa; wata mujalla da ake bugawa a kasar Jamus da ke binciko mahangar da al'adun al'ummomi, mai suna (fasaha da tunani) a cikin sabon bugunta ta kawo mahangar musulunci dangane da hakkokin dan adam. Mujallar ta buga wannan bayani ne dangane da mahangar addinin musulunci ta hanyar kawo misalai daga littafai da dama da marubuta musulmi suka rubuta kan matsayin musulunci dangane da hakkokin dan adam, inda ta kawo bayanan masana musulmi kan haka, wadanda suka dogara da fadar ubangiji ko kuma hadisan ma'aiki (SAW) da kuma bayyana wasu lamurra da suka faru a cikin tarihin musulunci a lokacin manzon Allah, da yadda ya bayyana matsayin musulunci kan hakkoki da daman a mutane, inda a kowane lokaci musulunci yana kare dukkanin hakkokin dan adam ne, bil hasali ma shi addini ne da ke bayyana ma dan adam hakkokinsa, tare da kiyaye adalci a cikin dukkanin lamurransa.
387322