IQNA

Za A Baje Kolin Kayan Tarihi Kan Irfani A Musulunci A New York

Bangaren kasa da kasa: Za a baje kolin wasu kayyakin tarihi da suke da dangantaka da irfani a musulunci a birnin New York na kasar Amurka.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran (Artdaily) cewa; daga farkon watan Mayu mai kamawa za a baje kolin wasu kayyakin tarihi da suke da danganataka da ilimin irfani a musulunci, wanda kuma baje kolin zai ci gaba har zuwa farkon Yuni. Daga cikin kayayyakin da za a nuna kuwa sun hada da wasu kayan tarihi na musulunci da suke da dangantaka irfani, da tarihinsu yake komawa zuwa ga karni na 13, wato kimanin kusan shekaru da suka gabata. Wasu daga cikin kayayyakin kuwa suna nuna akidar musulunci net a yin imanin da ubangiji guda daya ba tare da hada shi da wani abu a cikin bauta ba. Kamar yadda a cikin abubuwan akwai kasake na azurfa da kuma fitilu na zinari, gami da wasu takardu da ke dauke da rubuce-rubucen wakoki da dai sauransu.

387495