IQNA

Za A Fara Gudanar da Gasar Hardar Kur'ani A Kuwait

16:17 - April 14, 2009
Lambar Labari: 1764952
Bangaren kasa da kasa: Za a fara gudanar da gasar hardar kur'ani da tajwidi a karo na uku a yankin Almusi'a da ke cikin kasar Kuwait.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (Al-ra'ayi) ta kasar Kuwat cewa; sakatarrn kwamitin da ke kula da harkokin gasar kur'ani a kasar Kuwait Yusuf Sumai'i, ya sanar cewa an fara yin rijistar sunayen wadanda suke son su shiga cikin gasar, saboda haka wadanda suke son su yi rijista a halin yanzu kofa a bude take. Ya kara da cewa akwai sharudda da dole ne masu shiga cikin gasar su cika su kafin yi musu rijista, muhimmai daga cikinsu su ne; dole mutum ya hardace kur'ani, sa'anan kuma dole ya zama dan kasar Kuwait ne, rasa daya daga cikin wadannan abubuwa biyu zai hana yin rijista ga mutum, ya kara da cewa a wannan karon mutanen gari da suka cika wadannan sharudda za su iya shiga cikin gasar sabanin lokutan baya, inda aka shardanta cewa dole ne wadanda zai shiga gasar ko dai ya zama limami ne ko kuma mai kiran sallan. Ya kara da cewa an tanadi babbar kyauta ga wadanda suka lashe gasar.

387396

captcha